NATO ta gargadi Kungiyar Taliban
August 10, 2021Kungiyar tsaro ta NATO, ta yi kira ga Kungiyar Taliban da ta gaggauta tsagaita bude wuta a fadan da ta ke da gwamnatin kasar Afghanistan. Nato ta ce kasar na cikin matsanancin yanayi mai tattare da hadura da kuma manyan kalubale, a halin da ake ciki, ta ce karfin soji ba zai kawo mafita daga rikicin ba.
A jawabin Kungiyar, wani babban jami'inta, ya ja kunnen Taliban a game da yunkurin son karbe iko da karfin tuwo, ya ce, ba za a taba amincewa da duk wata gwamnati da za ta kafa ba koda ta sami nasara a yakin da ta ke.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a na shi bangaren, ya ce, Taliban ta aikata laifuka na kisan fararen hulan da wasu na'ukan cin zarafin bil'adama a yayin wannan rikicin..
Daruruwa sun rasa rayukansu a yayin da dubbai ke ci gaba da tserewa daga kasar tun bayan da mayakan Taliban suka kaddamar da hare-hare da karbe iko na manyan biranen kasar.