1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jamus ta dakatar da ayyukan raya kasa a Afghanistan

August 17, 2021

Jamus ta sanar da kawo karshen ayyukan raya kasa da take yi a kasar Afghanistan. Ministan Kula da Harkokin raya kasashe Gerd Mueller ya ce matakin ya biyo bayan kwace kasar da Taliban ta yi. 

Berlin | Bundesminister Gerd Müller | Bundestagssitzung
Hoto: Jens Krick/Flashpic/picture alliance

 

Tun daga ranar Lahadi lokacin da 'yan Taliban suka kwace iko da Afghanistan sun ci gaba da nanata cewa za su mutunta 'yancin mata kuma ba za su kuntata wa jami'in gwamnatin da suka hambarar ba.

Sai dai kuma 'yan kasar na nuna shakku da zullumin abin da ka iya faruwa, inda har aka samu yamutsi a yayin wani turmutsitsin ficewa daga kasar a filin jirgin saman Kabul. 

Minitsan kula da harkokin raya kasa na Jamus ya ce a yanzu sun mayar da hankali wurin ganin sun kwashe duk wani ma'aikacin agaji na Jamus da ke zaune a Afghanistan. Da ma dai rahotanni na nuna cewa hukumomin Jamus ba su riga sun fitar da kimanin Euro miliyan 250 da Jamus din ta ware don ayyukan raya kasa a Afghanistan a bana ba.