Kungiyar Taliban ta kai mummunan hari a Kabul
August 1, 2016Talla
Rahotanni daga babban birnin na kasar Afghanistan wato Kabul na cewa an ji karan tashin bam din a kusan duk fadin birnin da karan harbe-harben bindigogi a wurin da aka kai harin inda daga bisani tarin jami'an tsaro suka ja daga.
Bayan share awoyi ana fafatawa, hukumar 'yan sandar birnin na Kabul ta sanar da mutuwar maharan su uku. Amma kuma ta ce an samu mutuwar jami'in dan sanda daya a yayin da wasu hudu suka ji rauni.
Sai dai kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya sanar da cewa sojojin Amirka sama da 100 suka halaka wasu kuma sun ji rauni a cikin harin.