Kungiyar Taraiyar Turai da Iran sun amince sake tattaunawa
November 30, 2007Talla
Ƙungiyar Taraiyar Turai da Iran sun amince su buɗe sabon taro a wata mai zuwa kann shirin nukiliya na Iran.Babban kantoman kula da harkokin waje na ƙungiyar,Javier Solana ya gana da jakadan Iran wajen tattaunawar Saeed Jalili a birnin London,ya kuma baiyana tattaunawar cewa ta gamsar.Jamaa da dama dai sun ce wannan ganawa ita ce zata tabbatar ko Amurka da ƙawayenta zasu ci gaba da shirinsu na neman ƙarawa Iran takunkumi.Amurkan ta bukaci Iran da ta dakatar da shirinta na inganta uraniyum,Iran a nata ɓangare ta ce shirinta na samarda makamashi ne ga jamaarta.