1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

EU za ta bai wa Masar tallafin Euro biliyan daya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 13, 2024

A cikin yarjejeniyar bayar da tallafin, wajibi ne Masar ta ci gaba da martaba tsarin dimukuradiyya da hakkin 'dan adam

Hoto: Dati Bendo/EU Commission/dpa/picture alliance

Kungiyar tarayyar Turai EU ta yi alkawarin bai wa Masar tallafin kudi Euro biliyan daya domin tada komadar tattalin arzikinta da ke cikin mawuyacin hali.

Karin bayani:An yi kira ga EU da ta saka Masar a kokarin magance kwararar bakin haure

A watan Maris din da ya gabata ne Masar ta amince da karbar agajin dala biliyan 8 daga asusun bada lamuni na duniya IMF da kuma EU, a cikin tsarin dakile yadda bakin haure ke tsallakawa Turai ta barauniyar hanya, sannan kuma ta farfado da tattalin arzikinta.

Karin bayani:Za a ci gaba da rike kudaden ajiyar Hosni Mubarak a bankunan Turai

Haka zalika a cikin yarjejeniyar bayar da tallafin, wajibi ne Masar ta ci gaba da martaba tsarin dimukuradiyya da hakkin 'dan adam.