Tarayyar Turai ta kaste kudin taimakon Sabiya
May 1, 2026
Kungiyar Tarayyar Turai ta kaste kudin da aka ware domin ayyuka na musamman a kasar Sabiya karkashin shirin taimakon kasashe shida na yankin Balkans, saboda sauye-sauye masu janyo cece-kuce a bangaren na sharia na kasar da aka kaddamar.
Abin da ya janyo takaddama
Matakin ya biyo bayan kudirin majalisar dokokin Sabiya na amincewa da wata ayar doka mai cike da rudani ba tare da tattaunawa da masu gabatar da kara ba, ko alkalai, ko kuma hukumar Tarayyar Turai. Masu sukar dokar suna ganin ta kara wa shugaban kasa karfi kan alkaalai da cire su, da ma yi musu sauyi, lokacin da ake fuskantar manyan shari'u kan cin hanci a kasar ta Sabiya.
Karkashin shirin na Tarayyar Turai, da yanzu aka katse kasar ta Sabiya, an ware kimanin Euro bilyan 7.6 daga shekara ta 2024 zuwa 2027 domin ayyukan da za su bunkasa tattalin arzikin kasashen na yankin Balkans.