1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Tarayyar Turai ta sake sanya wa Siriya takunkumi

September 25, 2011

Jami'an tsaro sun ci gaba da gumurzu da masu boren nuna kyamar gwamnati a Siriya duk da takunkumin da Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya ma kasar

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin SiriyaHoto: picture alliance / dpa

Takunkumin da kungiyar Tarayyar Turai ta sanya wa Siriya ya fara aiki bayan da aka sami rahotannin cewa jami'an tsaro sun harbe wadansu fararen hula guda 13 ranar asabar, dukkansu a yankunan da ke kusa da birnin Homs. Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Switzerland sun sanya takukumin a sashen da ke kula da man fetur na kasar. Kungiyar ta EU ta haramta sayen hannayen jari da kuma aikar da takardar kudin kasar zuwa ga babban bankinta. Wannan mataki shine na bakwai a jerin takunkumin da Turai ta dauka domin hukunta gwamnatin shugaba Bashar al-Assad saboda murkushe masu boren nuna kyamar gwamnatin kasar wanda ya yi mafari tun a watan Maris din da ya gabata. A nata bangaren Siriya ta haramta shigar da kayayyaki da dama daga kasashen ketare, abun da ke shigowa yanzu, daga kayyakin da ba'a sarrafa ba sai kuma hatsi a kokarinta na yin tsimin ajiyar ta a kudaden musayar ketare

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita : Usman Shehu Usman