1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyin farar hula sun soki gwamnatin Nijar

Mahaman Kanta/PAWMay 26, 2015

Wakilan kungiyoyin farar hula 38 suka fitar da sanarwar da ta zargi gwamnatin da mulkin danniya bayan da ta ki sako 'yanuwansu da ta kame, da ma nuna halin ko in kula wajen kyautata rayuwar talakawa.

Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

A Jamhuriyar Nijar bayan tsare Musa Tchangari, da Nuhu Arzika, wasu daga ciklin shugabannin kungiyoyin kare hakkin dan adma da kare demokradiya. A yau shugabannin kungiyoyin faran hulla sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka zargi mahukuntan Nijar da mulkin kama karya.

"Bai yiwuwa dan kana rike da mulki, ka ce za ka yi wa talakawa wulakanci. Mulkin nan ba ka ci shi da karfi ba, a fiskar doka kake iko, kasa ta doka, kenan a fiskar doka za ka yi mulki kuma mu a Nijar, ba za mu yadda a yi mana mulkin danniya ba insha Allah"

Alhaji Mustapha Kadi, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin farar hullan da ke kare hakkin dan adam, wanda ya ke a matsayin kakakin kungiyoyi 38, da suka fitar da wannan sanarwa ya ke ba da wannan bayani, bayan da a cikin kakkausar murya suka kalubalanci gwamnatin Mouhamadou Issoufou, suka bukaci da a sako musu takwarorinsu da ke tsare Musa Tchangari da Nuhu Arzika, ba tare da wani bata lokaci ba ko gindaya wani sharadi.

'Yan majalisar dokoki ma ba su tsira ba

Shugabannin kungiyoyin farar hullan sun kuma kalubalanci 'yan majalisar dokoki a matsayinsu na wakilan talakawa, da cewa tun farkon bullar rikicin Boko Haram a cikin jihar Diffa ba su ce komai ba, alhali suna da hurumin yin magana da mahukunta su basu bayani a kai kamar dai yadda Mustapha Kadi ke cewa.

Musa Tchangari na tsare tare da Nuhu ArzikaHoto: DW/ Thomas Mösch

"Har yanzu ba mu ji inda 'yan majalisa suka ce za su kira firaminista, ko ministan tsaro ko na 'yan sanda ba, domin a gaya musu halin da ake ciki. Ana nan ana zargin mutane a bisa karya. Kuma su kansu sojojin sun bayyana cewa basu da kayan aiki kamar yadda Nuhu Arzika ya bayyana. Shugaban kasa ya yi ganawa da manema labarai, inda suka tambaye shi, sojoji sun ce ba su da isassun kayayyakin aiki, alahli kuma kullun ana cewa an kebe wani kasafin kudi na tsaro. Wannan mun yi bakin cikin abubuwa iri-irin da ke faruwa. "

Sanarwar ta su dai ta tabo abubuwa da dama, wadanda suka shafi kyautata rayuwar al'umma, wadanda suka hada da barkewar cutar sankarau abin da suke zargin hukumomin da yi wa rikon sakainar kashi tunda ba'a yi rigakafi ba yadda ya kamata

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani