Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun dakatar da yajin aikin gama gari
January 16, 2012Kungiyar kwadagon Najeriya ta sanar da janye yajin aikin gama gari da ta shiga, tare da amincewa da farashin Naira 97 a kan kowace litar man fetir da gwamnatin kasar ta sanar.
Sanar da janye yajin aikin da kungiyar kwadagon Najeriyar ta yi ,ya biyo bayan daukan lokaci mai tsawo da shugabanin gudanarwar kungiyar suka yi a Abuja, inda suka tattauna a game da mataki na gaba da ya kamata su dauka a kan wannan batu, musamman bayan jawabin da shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya yi wa al'uma, inda ya sanar da amincewa da rage farashin litar mai daga Naira 141 da gwamnatin ta sanra zuwa naira 97.
Sanar da janye dakatar da yajin aikin dai na kunshe ne a sanarwar da shugaban kungiyar kwadagon Najeriyar Comrade ya bayyana yana cewa:
Yace bisa ga abubuwa da ke faruwa ina sanar da dakatar da yajin aikin saboda dalilai da muka hango na iya sauya matakin da muka sanya a gaba.
Wannan mataki na kungiyar kwadagon Najeriyar ta dauka daya biyo bayan dakatar da zanga zanga ya nuna cimma matsaya a kan yajin aikin da ya gurgunta harkokin tattalin arzikin Najeriya.
Sakataren gudanarwa na kungiyar kwadagfon Najeriya Comrade Abbayo Nuhu Toro, ya bayyana dalilan da suka hango suka sanya su janye yajin aiki.
To sai dai sanin cewa an dade ana wa kungiyar kallon wace kan bari gwamnati ta yi amfani da ita a lokutan baya, da ma dagewar da ta yi a baya a kan lallai sai an koma kan farashin Naira 65, abinda ya sanya tambayar Comrade Abbayo Nuhu Toro Abdulwaheed Omar, ko mi ya sa suka amince da wannan farashi.
Kafin kaiga daukan wannan mataki da gwamnati ta sasauto saida shugaban Najeriya ya yi taro da gwamnonin kasar a daren Lahadi, inda suka amincewa da sasautowa bayan da mummunan yajin aikin ya gurgunta harkoki a Najeriya tare da sanya gwamnati tafka mummunar asara.
Shugaban Najeriyar dai ya yi alkawarin ci gaba da buda harkar man fetir din don baiwa 'yan kasuwa ikon su ci gaba da shiga don a taka da su, abinda kai staye ke nufin ci gaba da bin batun janye tallafin man fetir a cikin kasar, to sai dai ga Dr Jibo Ibrahim, shugaban kungiyar bunkasa demokradiyya ta Najeriya, wadanda suka kasance kan gaba wajen zanga zangar nuna adawa da janye tallafi na mai ra'ayin cewa su ba haka suke kallon al'ammuran ba.
Abin jira a gani shine ko sauran kungiyoyin kare hakin jama irin na masu yunkurin mammaye Najeriya zasu amince da matakin da kungiyar kwadagon kasar ta dauka da ma irin tasirin da hakan zai iya yi a wannan lamari, kasancewwa wannan shine yajin aiki mafi muni da aka fi daukan tsawon lokaci a tarihin Najeriyar, yajin aikin da ya hada kan al'ummar kasar tun bayan rigingimun zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar da ta gabata.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idriss
Edita:Yahouza Sadissou Madobi