1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KUNGIYYAR EU DA KASASHEN TEKUN BAHAR RUM KANN KASUWANCI.C

February 2, 2004
A yanzu haka Kungiyyar tarayyar Turai Wato Eu na tunanin aiwatar da gagarumin aiki na tallafawa kasashen da sukayi iyaka da tekun bahar rum wajen farfado da harkokin kasuwancin da kuma ciniki a kasashen ta hanyar saka jari daga kamfanonin kungiyyar har na dalar Amurka biliyon biyu da digo biyar. Kafin dai kashe wan nan kudi a can baya kusan shekaru biyu da suka gabata kungiyyar ta Eu ta kashe tsabar kudi har sama da dala biliyon biyar. Haka kuma bankin zuba jarin na kungiyyar ta Eu ya bayar da ranshen kudi har dala biliyon 17 ga kasashen na tekun bahar rum din daga shekara ta 1974 izuwa 2001,don aiwatar da ayyuka iri daban daban. Wadan nan kudade dai an kashe su ne wajen farfado da harkokin masana,antu da kuma kamfaninnika a wasu daga cikin kasashen. Ana kuma sa ran cewa kudin da kungiyyar ta Eu zata kashe a wan nan shekara zaifi ne a fannoni da suka hada da gine ginen abubuwan more rayuwa da harkar lafiya da ruwan sha da kuma farfado da harkar ilimi. Wan nan dai manufa ta tallafawa kananan masaa,antun kasashen na tekun bahar rum an cimma masa bisa yarjejeniya a tsakanin kasashen goma sha biyu da kungiyyar ta Eu a wan nan shekara da muke ciki. Kasashen sun hadar da Algeria da Cyprus da Israel da Jordan da Lebanon da Malta da Morocco da Palestine da Syria da Turkey da kuma Tunisia. Bisa rahotanni kuwa da suka iso mana wan nan mataki da kungiyyar ta Eu ta dauka ya samu karbuwa ne bayan wani taro da aka gudanar na tallafawa kananan masana,antu masu zaman kansu na wadan nan kasashe daga kasashen ketare. Taron wanda aka gudanar a birnin London na kasar Biritaniya makon daya gabata,ya samu halartar hamshakan yan kasuwa daga fannoni daban daban na rayuwar bil adama har guda 150. A yanzu haka dai kungiyyar ta Eu ta cimma yarjejeniya a tsakanin da yawa daga cikin wadan nan kasashe goma sha biyu kann cire haraji na abubuwan da da zai shiga tsakanin su na hada hadar kasuwanci,a wani yunkuri na taimakawa kananan masana,antun yankin samun ci gaba mai dorewa a cikin kasashen nasu. Wan nan dai sabon matakin da kungiyyar ta Eu ta dauka da kuma ire iren tarurrukan da aka gudanar a birnin London dana Casablanca,ya haifar da sake wani taron a birnin Marseilles na Faransa a watan nan da muke ciki sai kuma na gaba da ake sa ran yinsa a Alexandria na kasar Masar a watan yuni. A hannu daya kuma rahotanni sun nunar da cewa tarurrukan da aka gudanar a baya da wadanda za,a gudanar a nan gaba ana shirin yin sune bisa manufar cimma wan nan buri da kungiyyar ta Eu ta sako a gaba na farfado da harkokin masana,antu da kuma kamfaninnikan kasashen na tekun bahar rum din.