1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An gano kura-kurai a rijistar masu zabe

Uwais Abubakar Idris RGB
April 14, 2022

Hukumar INEC ta nuna damuwa bayan ta gano wasu kura-kurai a takardun rijistar kashi 45 cikin dari na mutanen da suka yi sabuwar rijistar jefa kuri’a a zaben kasar da ke tafe.

Nigeria Vizepräsident Yemi Osinbajo (L)
Hoto: Press Office Yemi Osinbajo

A Najeriya Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato INEC ta nuna damuwa a kan abin da ta gano na cewa kashi 45 cikin dari na mutanen da suka yi sabuwar rijistar jefa kuri’a ta lalace a dalilai mabambanta, ana saura watanni biyu a kama aikin rijistar don zaben da za’a gudanar a shekarar 2023.

Bayan kwashe watanni bakwai tana aikin sabunta rijistar masu jefa kuri’ar ne hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya ta bayyana gano cewa kashi 45 na wadanda suka yi sabuwar rijistar duka lalatacciya ce, domin kuwa ba za’a iya amfani da ita a babban zaben Najeriyar ba. Adadin da ya nuna a tsawon wannan lokaci mutane milyan 1.8 ne rijistar da suka yi aka buga katunansu.

An gano kura-kurai a rijistar masu kada kuri'aHoto: AP

Matsaloli na yin rijista fiye da sau daya da masu rijistar suka yi saboda bullo da rijista ta yi da kanka ta yanar gizo ne dai ta haifara da hakan kamar yadda shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar. Tuni ‘yan siyasa da kungiyoyin farar hula da ke sa ido a kan zaben suka baiyana damuwarsu a kan abin da hukumar zaben ta bayyana sanin cewa lokaci na neman kure mata a wannan muhimmin aiki da dole sai da shi za’a iya gudanar da zabe.

Sanin cewa saura watanni biyu ya rage a kamalla aikin rijistar masu jefa kuri’a a bisa doka a Najeriya ko za’a iya gyara wannan kuskure har mutanen su samu yin rijista a zaben don kaucewa fuskantar matsala. Hukumar zaben na da zummar yi wa ‘yan Najeriya miliyan casa'in don su yi zabe a shekara mai zuwa, abin da ya nuna kari daga miliyan mutane miliyan saba'in da biyu da aka yi wa rijista a zaben 2019, ko hukumar za ta kai ga cimma nasara, wannan lokaci ne zai tabbatar.