1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kura ta lafa a ƙasar Kenya

MamaneAugust 29, 2012

Kungiyoyin kare haƙƙin bil Adama na nuna fargaban ga rikicin da ya ɓarke a Kenya biyo bayan kisan wani shehin malami

Duk da cewa kura ta lafa sosai a birnin Mombasa inda rikici ya barke biyo bayan kisan da a kawa wani fitaccen shehin malami a ran Littanin da ta shude, abunda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 4 daga ciki har da 'yan sanda ukku da kuma farar fula daya.Yanzu haka shuwagabanin addinai musulmai da krista sun soma fadakar da jama'a a wani matakin kaucewa duk wani tashin tashina da ke da nasaba da rikicin addini. Kasar ta Kanya inda mabiya addinin krista keda babban rinjaye ta sha samun kanta a cikin rikice-rikicen kabilanci da addini abunda ya tayar da hankalin kungiyoyin kare hakin bil adama na ciki da wajen kasar kamar yadda Ben Rawlence daga kungiyar kare hakin nbil adama ta Human Rights Watch reshen Kanya ke cewa.

"Kisan da akayi wa Abud Rogo laifi ne, da ba mu san wanda ya aikata ba. Amma kungiyar Human Right Watch da sauran kungiyoyin kare hakkin bil Adama na Kenya, na nuna damuwa kan bacewa da hallaka masu jiran hukuncin kisa da wadanda ake zargi da aiyukan ta'adanci. Shi ne mutun na biyu da aka hallaka kuma na shida daga wadanda ake zargi da aiyukan ta'addanci da su ka bace a wannan shekara. Akwai gawa daya aka aka samu kusa da wajen shakatawa na kasa, a watan Maris. Wannan abubuwa ne da su ke jawo damuwa, gwamnatin Kenya ta nuna damuwa abun da ya sa aka kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa da hukumar kare hakkin iol Adama ta Kenya, da 'yan sandan domin binciken kisan Abud Rogo."

Tun can farko dai hukumomin kasar da ma Amirka na zargin malamin addinin da hada baki da 'yan kishin islaman Shebab na Somaliya gurin kai hare hare a ofishin jakadancin Amirka da ke Mombasa a shekara ta 1998 wanda ya yi sanadiyar murtuwar a kalla mutane 240.
A lokacin da ya bayani a game da wadanda a ke zargi da ayukan ta'addanci a kasarjami'in na kungiyar kare hakin bil adaman cewa ya yi, wadanda ake zargi da aiyukan ta'addanci da aka cafke na nuna damuwa kan makomar rayuwarsu:

Hoto: dapd

"A gaskiya wadanda su ke fuskantar irin wadannan tuhume-tuhume a kotunan Kenya, na cikin damuwa. Na yi magana da wani lauya wanda ya ke wakiltan mutanen da ya tabbatar mini da haka. Duk masu haka ko 'yan sintiri ko mutane masu daukan doka a hanunsu saboda haushi, su ma jami'an tsaro, gaskiya abun damuwa ne."

Hukumomin kasar ta kenya na amfani ne da wata doka ta musamman da gwamnatin ta zartar ta yaki da aukan ta'addanci domin cin zarafin jama'a da kuma ramuwar gaya a kan wadanda basu san hawa ba balle sauka. Kawo yanzu dai shugaban kasar Mwai Kibaki ba ce komai ba a dangane da hargatsin da ya taso a farkon makon nan yayinda paramiyansa Raila Odinga ya tabbatar da daukar matakai da kuma gudanar da bincike a kan abuda ya faru.

Hoto: Getty Images

Mawallafa: Mohamed Khelef/ Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi