1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Kurdawa sun zargi Iran da kai hari a cibiyarsu da ke Iraki

Mouhamadou Awal Balarabe
January 21, 2026

Jami'iyyar Kurdawa ta PLK ta ce harin ya samo asali ne daga kiran da ta yi wa 'yan Iran na gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma mallakar rundunar sojoji da ta samu horon soji.

Kurdawan Iran sun shafe shekaru suna gagwarmayar 'yantar da yankinsu
Kurdawan Iran sun shafe shekaru suna gagwarmayar 'yantar da yankinsuHoto: picture-alliance/dpa

Wata jam'iyyar adawa ta Kurdawan Iran da ke da hedikwata a Iraki ta zargi fadar mulki ta Tehran da kai hari kan ofishinta da rokoki da kuma jiragen sama marasa matuka, inda ta kashe daya daga cikin membobinta tare da raunata wasu biyu. Wani babban jami'in PLK ya shaida wa AFP cewar harin ya samo asali ne daga kiran da jam'iyyar ta yi wa 'yan Iran na gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma saboda tana da rundunar sojoji da ta samu horon soja.

Ita dai jam'iyyar neman 'yancin yankin Kurdistan da aka kafa a shekarar 1991 a Iran, ta kunshi mayakan da suka yaki 'yan kungiyar ta'addanci ta IS a kasar Iraki. Dama dai tun shekarun 1980, lokacin da Iraki ke karkashin mulkin Saddam Hussein, jam'iyyun adawa da dama na Kurdawan Iran sun kafa sansanoninsu a Iraki.