Brexit: 'Yan majalisa za su kada kuri'a kan ficewa daga EU
October 19, 2019Talla
'Yan majalisar dai za su kada kuri'an bisa nuna amincewa ko akasin hakan da daftarin na mista Johnson. Firaiministan da ya dage kan ficewar kasar koda ba da yarjejeniya ba, yana neman goyon bayan 'yan majalisar a matakin da zai bai wa Britaniyyan damar raba gari da kungiyar ba tare da an fuskanci tarnaki ba. A ranar talatin da daya ga wannan watan na Oktoba, wa'adin ficewar ke cika.