Majalisar Amirka ta amince da tsige Shugaba Trump
December 19, 2019Talla
Kuri'ar wacce ta kasance ta tarihi, a yanzu majalisar dokokin Amirka ta tabbatar shugaba Donald Trump ya aikata laifi. Laifuka biyu ne dai aka tuhume shi da aikatawa.
Laifukan sun hada da batun barazana ga abokin hamayya bisa hadin baki da wata kasa da kuma hana ma'aikatan fadar White House da hada baki da wata kasar. Kuri'u 230 sai kuma 197 suka ki amincewa.
Shugaba Trump ya kasance shugaban Amirka na uku da aka taba kada wa irin wannan kuri'ar ta tsigewa.
Sai dai yanzu za tura batun izuwa majalisar dattawa. Shi dai Trump ya yi watsi da kuri'a inda yake saran tsallake rijiya a majalisar dattaijai.