1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump ya fuskanci kakkausar suka daga 'yan Demokrat

Abdoulaye Mamane Amadou
August 18, 2020

A ci gaba da taron jam'iyyar Demokrat wasu manyan 'yan siyasa ciki har na 'yan jam'iyyar Republican sun caccaki shugaba Donald Trump, a yayin da Michelle Obama ta bukaci Amirkawa da su zabi Joe Beiden

Parteitag der Demokraten
Hoto: picture-alliance/dpa/Democratic National Convention

Michelle Obama da ke jawabi a yayin bude taron da jam'yyar Demokrat ke gudanarwa yanzu haka don tsayar da Joe Beiden da Kamala Harris a matsayin 'yan takarar da za su kalubalanci Donald Trump, ta bukaci Amirkawa da su zabi Joe Beiden a zaben ranar uku ga watan Nuwamban wannan shekara.

Ta ce "A duk lokacin da Amirkawa suka karkata zuwa fadar White House don samun mafita kan wata matsalar, sukan fuskanci rudani da rarrabuwar kai da rashin fahimta" a yayin jawabin da Michelle Obama ta yi na tsawon mintoci 20.

Bangarori da dama dai sun gabatar da jawabansu a yayin taron ciki har da 'ya 'yan jam'iyyar Republican da kuma dangin George Floyd bakar fatar nan da wani dan sanda farar fata ya yiwa kisan gilla a kasar Amirka.