1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon sarkin Kuweit

Mahmud Yaya Azare LMJ
September 30, 2020

Yarima Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah ya zama sarkin Kuwait, bayan rasuwar dan uwansa marigayi Sarki Sabah al-Ahmad Al-Sabah.

Kuwait | Neuer Emir | Sheikh Nawaf Al Ahmad Al Sabah
Sabon sarkin Kuwait Sheikh Nawaf Al Ahmad Al Sabah ya yi ranmtsuwar kama aikiHoto: Jaber Abdulkhaleg/AP Photo/picture alliance

Yarima Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah da ke da shekaru 83 a duniya, yayi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon sarkin kasar ta Kuwait ne, a daidai lokacin da shuwagabannin kasashen duniya ke ci gaba da aike wa da sakon ta'aziyyarsu, sakamakon rasuwar marigayi tsohon sarkin kasar Kuwait din Sabah al-Ahmad Al-Sabah da ya rasu a ranar Talatar 29 ga watan Satumbar da muke ciki,  yana da shekaru 91 a duniya. KUma an rantsar da Yarima al-Ahmad Al-Sabah ne a karkashin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

Karin Bayani:  Bude zaman taron neman lafiyar kasar Yemen a Kuwait

Kakakin fadar masarautar ta Kuwait, Sheikh Ali Jarrah Al-Sabah ya jajantawa 'yan kasar tasa da ma sauran kasashen duniya, kan rasuwar marigayi Sarki Sabah al-Ahmad Al-Sabah da ya rasu a wani asibiti a Amirka, bayan ya sha fama da jinya, ya na mai bayyana marigayin sarkin da cewa ya karar da rayuwarsa ne wajen hidimtawa 'yan kasarsa da gabatar da ayyukan agaji ga mabukata a ko ina, gami da fafutukar ganin an samar da zaman lafiya da ci-gaba a fadin duniya, wanda hakan ta sa ya cancanci samun kyakkywar adu'ar dacewa a lahira.
Gwamnatin kasar dai ta ayyana zaman makoki na kwanaki 40 da rufe ofisoshin gwamnati da ma'aikatu na tsawon kwanaki uku saboda wannan rashin. Marigayin Sarki Sheik Sabah al-Ahmad al-Sabah dai na shan yabo matuka, saboda salon iya mulkinsa da kokarinsa na shiga tsakani domin sasanta rikice-rikice a kasashen Larabawa, musammama rikicin kasar Qatar da kasashen yankin Gulf.

An yi jana'izar marigayi sarkin Kuwait Sheik Sabah al-Ahmad al-SabahHoto: Raed Qutena/dpa/picture-alliance

Karin Bayani: An mayar da kasar Qatar saniyar ware

Tuni shugabannin kasashen duniya da kungiyoyi, suka fara aika sakon ta'aziyyarsu, suna masu bayyana marigayin sarkin a matsayin mai son hadin kan al'umma da zaman lafiya, wanda ya bayar da gudunmuwarsa a fannoni da dama na rayuwa da ba za a taba mantawa da shi ba. Mariyagayin wanda ke mulkin Kuwait tun a shekarar 2006, shi ne sarki na 15 a gidan sarautar kasar da suke rike da ragama shekaru kusan 250 da suka gabata. Duk da cewar yana da da, sai dai kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, kaninsa da ke bi masa a shekaru ne zai gaje shi. Yayin jawabinsa bayan ya sha ranstuwar karbar mulkin, sabon sarkin Kuwai din Yarima Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah  ya yi alkawarin ci gaba daga inda marigayin ya tsay.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani
Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW