1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwalara ta hallaka mutane a Habasha

November 30, 2023

Kasar Habasha ta fuskanci ambaliya a baya-bayan na fama da matsalar cutar kwalara a yankin gabashinta. Cutar ta kashe mutane fiye da 20, ana kuma gargadin abin na iya bazuwa.

Wasu da ke fama da cutar Kwalara
Wasu da ke fama da cutar KwalaraHoto: DW

Akalla mutane 23 ne rahotanni ke cewa cutar kwalara ta yi ajalinsu a gabashin kasar Habasha, yankin da ya fuskanci ambaliyar ruwa a baya-bayan nan.

Kungiyar taimako da kare hakkin kananan yara ta Save the Children wadda ta ba da alkaluman wadanda suka mutun, ta ce akwai yiwuwar cutar ka iya bazuwa zuwa wurare da dama a yankin.

Kasar ta Habasha da ke makwabtaka da Kenya da Somaliya, sun fuskanci ruwan sama kamar da bakin masaki da ya haddasa ambaliyar da ta yi sanadin salwatar rayuka a yankin kusuwar Afirka.

Save the Children din ta kuma ce cikin makonni biyu da suka gabata, akwai mutum 772 da suka kamu, kuma 23n suka mutu.