1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalara ta salwantar da rayuka a Sudan

August 14, 2025

Akalla mutane 40 ne bayanai ke tabbatar da mutuwarsu a yankin Darfur na kasar Sudan, sakamakon barkewar annobar cutar kwalara.

Asibitin Tawila a Sudan dauke da masu fama da kwalara
Asibitin Tawila a Sudan dauke da masu fama da kwalaraHoto: Mohammed Jamal/REUTERS

Kungiyar likitoci masu agaji ta Doctors Without Borders ta ce barkewar annobar na daga cikin tashin hankali mafi girma da al'ummar kasar ke fuskanta, tun bayan barkewar yaki a kasar tsakanin dakarun gwamnati da kuma rundunar kar-ta-kwana ta RSF.

Shugaban kungiyar likitocin a Sudan Tuna Turkmen, ya ce lamarin na neman gagarar kundila, kasancewar cutar na yaduwa cikin hanzari a kasashen Chadi da Sudan ta Kudu wadanda ke makwabtaka da Sudan.

Kungiyar ta doctors Without Boarders ta ce ta kula da marasa lafiya akalla 2,470 a wannan wata na Agusta daga cikin mutane dubu 99,700 da suka kamu da cutar ta kwalara.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW