1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwale-kwale ya kife da 'yan ci rani 46

Abdul-raheem Hassan
June 7, 2018

Akalla bakin haure 16 sun mutu a ruwa, bayan da kwalekwale dauke da 'yan kasar Habasha 46 ya nitse a kusa da gabar Tekun Yemen.

Jemen Migranten
Hoto: AFP/IOM

Wadanda suka tsira daga hatsarin sun ce lamarin ya faru ne sakamakon rashin sanya rigunan kariya. Masu ayyukan ceto sun ce kwale-kwalen na dauke da kusan 'yan ci rani 100, wandanda suka tashi daga tashar jirgin ruwa ta Bosaso a Somaliya da nufin Zuwa kasar Yemen neman aiki.

Hukumar kula da kauran jama'a ta duniya IOM ta ce a karshen makon da ya gabata wasu mutane 112 sun mutu bayan da kwale-kwale ya kife da su a Tekun Tunisiya.