Kwale-kwale ya nitse da mutam 100 a Kwango
October 9, 2021Talla
Hukumomin agaji sun gano gawarwaki 61 daga ranar Llitinin zuwa Talata, sannan ana ci gaba da neman wasu mutane 60 da suka bace, kamar yadda Nestor Magbado, kakakin gwamnan lardin Mongala da ke Arewa maso yammacin kasar ta Kwango ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
Hukumomi sun ce hadarin kwale-kwalen na da nasaba da cunkoson kaya da jama'a da kuma rashin kyawun yanayi. Wannan shi ne karo na baya -bayan nan a jerin hadurran ruwa a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, inda mutane kan yi tafiye -tafiye a cikin jiragen ruwa masu yawa da marasa lafiya.