Kwamandojin Boko Haram sun mika wuya
April 20, 2018Talla
Wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram su 7 ciki har da mace guda, sun ajiye makamansu tare da mika wuya ga rundunar Sojin Najeriya. Su dai kwamandojin da suka tabbatar da janyewa daga kungiyar Boko Haramun din a Maiduguri babban birnin jihar Borno, sun ce sun yi hakan ne don shiga shirin afuwa da gwamnatin tarayya ta fito da shi. Kamar yadda suka shaida wa wakilin DW a yankin Al Amin Suleiman Muhammad.
Babban kwamandan Operation Lafiya Dole Manjo Janar Nicolas Rogers ya yi kira ga sauran mayakan da su ke daji, da su fito su mika wuya a shirye gwamnati ta ke ta yi musu afuwa tare da sama musu ayyukan yi.