1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe kwamandojojin Hamas a Gaza

Abdul-raheem Hassan
November 26, 2023

Yayin da ake sa ran sako karin mutane da ke tsare a hannun Isra'ila da Hamas a rana ta uku a yarejejniyar tsagaita wuta a Gaza, sojojin Isra'ila sun harbe wani manomi Bafaladsine har lahira da wasu mutane bakwai.

Sojojin Isra'ila a asibitin Al-Shifa da ke GazaHoto: AFP

Kungiyar Hamas ta tabbatar da mutuwar hudu daga cikin kwamandojinta a zirin Gaza ciki har da mai kula da arewacin yankin, ko da yake kungiyar ba ta bayyana lokacin da aka kashe mata kwamandojin ba.

Babu martani nan take daga bangaren Isra'ila kan sabon harin da ya kashe Faladsinawan, kuma babu tabbas ko matakin zai shafi matakin farko na yarjejeniyar sako 'yan Isra'ila 50 da Faladsinawa 150 da ke tsare cikin kwanaki hudu na dakatar da barin wuta da aka cimma.

Gwamnatin Isra'ila ta sanar da karbar jerin sunayen karin mutanen da za a sake bayan da ta sako Faladsinawa 39 a ranar Asabar.