Alhakin mutuwar yahudawa 45 yayin bauta na kan Netanyahu
March 6, 2024Kwamitin bincike kan mutuwar 'yan Isra'ila 45 a wurin bauta a shekarar 2021, ya dora alhakin faruwar lamarin ga firaministan kasar Benjamin Netanyahu, sakamakon sakacin da ya nuna a kai.
Karin bayani:Isra'ila ta amince da sake tattaunawar sulhun tsagaita wuta a yakin Gaza
Bayan tattara shaidu guda 213, kwamitin mai mutum uku, ya gano cewa wurin bautar yana da tarin matsaloli da ke bukatar gyara amma Mr Netanyahu ya gaza daukar matakan da suka dace, kasancewar an sha tunatar da shi da ministocinsa da ma mukarraban fadarsa da jagororin addini, har ma da shugaban 'yan sandan kasar, game tabarbarewar wurin ibadar amma shiru.
Karin bayani:Isra'ila ba ta son Falasdinu ta samu 'yanci
Dubban Yahudawa ne suka yi tururuwa don gudanar da ibada yayin ziyarar kabarin wani babban jigon addini, daga nan turmutsi da turererinya suka haddasa mutuwar mutane 45 a shekarar ta 2021.