Kwamitin Lord Robin Butler na Britamniya kan iraq ya mika rahoto
July 14, 2004Pm Tony Blair na britaniya a bisa wannan rahoton dai ya wanke shi tas ko babu sabulu na rade radin cewa wai yayi karin gishiri a dangane da hujjojin da suka sanya kasar ta shiga yaki da iraq wanda yayi sanadiyar kifar da gwamnatin Sadam Hussain a shekarar bara .A yayin da wannan rahoto ya bayyana gazawar gwamnatin kasaar na gudanar da bincike mai zurfi wanda zai bayar da halarcin wannan yakin sai bayanai na sirri suika bige da samun kura kurai a cikin su .To sai dai a kare martabar gwamnatinsa Pm Blair a zauran majalisar dokokin kasar yace koda kuwa an tabbatzar da wadannan kura kurai babu shakka kawar da sadam daga madafan ikon kasar yazo daidai bisa laakari da yarda yake cin zarafin yan kasar baki daya .To sai dai wannan rahoto zai kasance wani mizani ne na auna kimar Pm da kuma gwam,natinsa a wani zabi na cike gurbi da zaa gudanar a makon gobe a cikin kasar .A daura da haka dai a bisa siyasar kasar kuwa a yanzu ta tabbata cewa kimar da Pm Blair keda ita a baya a yanzu ta zube baki daya Bayan kasancewa a madafan ikon kasar na kusan shekaru 7 bayan kuma shafe kusan shekaru 18 a matsayin dan adawa a siyasar kasar a yanzu Jamiyyar labor na tunanin tsayar da Ministan kudi na kasar ya zama dan takarar neman Pm idan har jamiyyar na neman ta sami karbuwa a fadin kasar ta britaniya a halin yanzu .Pm Tony Blair wanda ya kasance dan kanzakin shugaba Bush a yakin Iraq wanda yayi sanadiyar kifar da gwamnation sadam Hussain a iraq ya kuma aike da karfin sojin da suka tasamma sama da dubu 45 a cikin kasar domin yaki da sAdam Hussain ..A halin yanzu dai Pm ya dauki nauyin cewa shine keda laifi a wadannan kura kurai kuma ya dauki matakai na jan raayin jamaaar kasar wajen tabbatar da hallarcin wannan yakin da kasar ta shiga a iraq .Bugu da kari ya kuma tabbatar da samun nasara a duk zaben da zaa gudanar a kasar bisa jagorancin jamiyyarsa ta labor .Tony Blair dai ya kasance Pm a yayin da yake dan shekaru 43 da haihuwa a shekara ta 1997.An sake gudanar da wani sabon zabe a shekara ta 2001 inda Pm ya sami nasara a karo na biyu a siyasar kasar .Shi dai Pm kwararen lauya ne wanda ya kammala karatunsa a jamiar Oxford .Tun kafin ya cika shekaru 30 Pm Blair ke taka rawar siyasar kasar wanda a shekara ta 1992 ya taba zama dan majalisar dokokin kasar .Ya dai dauki matakai na gyara a fadin kasar baki daya sai dai kuma ya gaza jan raayin yan kasar dasu sdaina anfani da kudaden Pam zuwa Euro .Tun daga Gwamnatin Bill Clinton na Amurka Pm Blair ke karfafa huddar jakadanci da Amurka har kawo yanzu ga Shugaba Bush Yana da Matarsa mai suna Cherie Booth wacce itama kwararriyar lauya ce kuma suna da yaya hudu a halin yanzu .