1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhu ya kasa cimma matsaya game da yin tir da ƙasar Siriya

April 28, 2011

Jakadan Siriya a Majalisar Ɗinkin Duniya ya nuna farin cikinsa game da rashin amincewa da shawarar yin tofin Allah tsine ga gwamnatinsa.

Gwamnatin Siriya na ɗaukar matakan ba sani ba sabo kan masu boreHoto: AP

Ƙoƙarin da ƙasashen Turai suka yi na neman kwamirin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadai da Siriya dangane da matakan murƙushe masu zanga-zangar lumana, ya ci-tura. Ƙasashen Jamus, Faransa, Birtaniya da kuma Portugal suka gabatar da daftarin na neman yin tir da gwamnatin Siriya. Amma Rasha da China suka yi watsi da shi. To sai dai an jiyo jakadiyar Amirka a Majalisar Ɗinkin Duniya Susan Rice ta yi kira ga gwamnatin birnin Damascus da ta canja alƙibla.

"Gwamnati ta na kira ga shugaba Bashar Assad da ya canja alƙibla yanzu, kana ya saurari koke koken mutanensa. Muna kira ga gamaiyar ƙasa da ƙasa da ta mayar da martani ga wannan ta'asa ta murƙushe masu zanga-zanga kana ta ja kunne masu hannu a matakan keta haƙin bil Adama."

Shi kuwa jakadan Siriya a Majalisar ta Ɗinkin Duniya Bashir Jaafari murna yayi da rashin cimma daidaito yana mai cewa.

"Haƙansu bai cimma ruwa ba a ƙoƙarin yin amfani da halin da a ke ciki a Siriya don cimma burinsu. Godiya ta tabbata ga fahimtar da ɗaukacin masu basira a kwamitin suka nuna."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi