Kwamitin Sulhu ya yi tir da furucin shugaba Ahmedi Nejad na kyamar Isra´ila
December 10, 2005Kwamitin sulhu na MDD ya shiga sahun kasashen duniya wajen yin tir da furucin da shugaban Iran Mahmud Ahmedinejad yayi na nuna kyamar Isra´ila. A cikin wani kuduri da ya zartas kwamitin sulhu ya ce haramun ne wata membar kwamitin ta yi barazana ga ´yanci da wanzuwar wata kasa. A ranar alhamis da ta gabata shugaba Ahmedinejad ya kwatanta Isra´ila da wata cutar cancer sannan ya ce kamata yayi a mayar da kasar ta bani Yahudu a wani yanki dake tsakanin Jamus da Austria. Hakazalika shugaban ya yi suka da yadda ake ba da muhimmanci ga kisan kare dangi da gwamnatin Nazi ta yiwa Yahudawa a lokacin yakin duniya na biyu. A halin da ake ciki ma´aikatun harkokin wajen biranen Berlin da Vienna sun ba da takardun sammaci ga jakadun Iran dake kasashen su don nuna adawa da furucin na shugaba Ahmedinejad.