Kwanaki 100 da fara zanga-zanga a Iran
December 28, 2022Daruruwan mutane a birnin Mashad sun tari aradu da ka inda suka fita zanga-zangar nuna fushinsu da matuwar Mahsa Amini. Kwanaki 100 da suka gabata ke nan lamarin dake zama dan Ba na fara zanga zangar adawa da Hijabi data zama gama gari a fadin kasar, wacce ta tilasta wa mahukunta rufe makarantu da daukar tsauran matakan dakile boren ta hanyar amfani da karfin da ya wuce kima da jami‘an tsaro suka yi ta yi wa masu zanga-zangar, lamarin da ya kai ga halakar masu zanga-zangar fiye da 500 da daure wasu dubban.
Duk da jingine dokar tursasa wa mata sanya Hijabi da soke hukumar ‘yan sandan da‘a da ake ce wa Hisbah a kasar, gami da tauna aya don tsakuwa ta shiga taitayinta da mahukuntan na Iran suka yi, wajen sanya hukuncin kisa ga masu zanga-zangar adawa da gwamnati, wacce ta kai ga zartar da ita kan wani matashin likita.
Sai dai hakan bai sanya masu adawa da gwamnatin sarewa ko janye manufar fara zanga-zangar ba, wacce ta rikide zuwa zanga-zangar neman ganin bayan mulkin kama karya na juyin juya halin musulunci, kamar yadda wadannan masu zanga-zangar da suka fita a daren jiya ke fadi.
Mahukuntan Iran da magoya bayansu dai na daukar masu zanga-zangar da ‘yan barandan kasashen Amurka da Isra‘ila, wadanda a ta bakinsu bayan sun kasa tankwara ta ko hana ta tabukawa, sakamakon hare-hare da kulla mata makarkashiya. Yanzu suke kokarin wargaza ta ta hanyar amfani da wasu wadanda take siffanta su da maciya amanar kasa. Don haka ne ma shugaban addinin kasar Ayatullah a ranar da ake jana‘izar jami‘an tsaron kimanin 11 da suka mutu a yayin fito-na-fito da masu zanga-zanga, ya jinjina wa matakan da gwamnatin Shugaba Ibrahim Ra‘isi ke dauka na abun da ya kira ceton kasa daga makiyanta da makiya addnin musulunci.