1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na gasa wa Rasha aya a hannu-Wolodymyr Selensky

Abdoulaye Mamane Amadou Sulaiman Babayo
December 20, 2022

Shugaba Wolodymyr Selensky ya yi ikrarin cewa dakarun Ukraine na gasa wa takwarorinsu na Rasha aya a hannu a ci gaba da yakin da suke gwabzawa tun farkon wanna shekara.

Volodymyr Zelensky
Hoto: AFP/Getty Images

A cikin wani jawabinsa na kowane dare ga 'yan kasar, Shugaba Selensky, ya ce fiye da sojin Rasha 900 ne suka kwanta dama a yakin, yana mai cewa nan da wasu 'yan lokuttan za su kasance dubu daya.

Wolodymyr Selensky ya zargi Rasha da bata lokaci wajen yakin da ke ja mata mummunan asarar dukiyoyi da na rayuka, duk da kokarin da take na kare manufofinta a yankin.

A ranar 24 ga watan Febrairun wannan shekarar ne Rasha ta kaddamar da mamaya kan makwabciyarta Ukraine, inda a wannan Talatar yakin na Ukraine ke cikja kawanaki 300.