1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango da Ruwanda za su sanya hannu kan yarjejeniya

April 25, 2025

Sakataren harkokin wajen Amirka, Marco Rubio zai jagoranci sanya hannu kan wata yarjejeniyar a tsakanin kasashen Ruwanda da Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango.

USA Washington 2025 | Außenminister Rubio empfängt katarischen Premier Al Thani
Hoto: Aaron Schwartz/Sipa USA/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amirka, Marco Rubio zai karbi bakuncin sanya hannu kan wata yarjejeniyar a tsakanin kasashen Ruwanda da Jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango, bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma. Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce Rubio zai rattaba hannu kan takardar ka'idoji tare da ministocin harkokin waje kasashen biyu.

Karin bayani: M23: Qatar ta sulhunta Kwango da Ruwanda

Tun dai a ranar Larabar da ta gabata ce dai, Jamhuriyar dimukuradiyar Kwango da kuma 'yan tawayen M23 suka bayyana cewa sun amince da dakatar da fadaa gabashin Kwango yayin da suke kokarin ganin an cimma matsaya ta dindindin. Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a rikicin da ya barke a kan iyakar kasashen biyu tun  watan Janairun wannan shekarar.