1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango da Rwanda sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya

Binta Aliyu Zurmi
December 5, 2025

Kwango da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta marawa baya a Washington.

USA Washington D.C. 2025 | Trump bei Unterzeichnung des Friedensabkommens mit Ruanda und der DR Kongo
Hoto: Andrew Caballero-Reynolds/AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya taya shugabannin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango Felix Tshisekedi da takwaransa na Ruwanda Paul Kagame murna biyo bayan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da suka amince da ita a fadar White House.

Shugabannin biyu da suka jima ba sa ga maciji a tsakaninsu sun sanya hannu kan yarjejeniyar da ke da nufin kawo karshen rikici a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, duk da cewa ana ci gaba da gwabza kazamin fada a gabashin Kwongo tsakanin sojoji da mayakan sa-kai.


Matakin a cewar Trump, zai bude wa Amurka da kamfanoninta damar saka hannayen jari a fannin hakar ma'adinan a Kwango. 

Trump ya gana da Tshisekedi da Kagame a wasu tarurruka daban-daban kafin hawa kan teburin sa hana don cimma wannan yarjejeniyar mai muhimmanci.

Sai dai shugabannin na Ruwanda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ba su kalli juna ba, kazalika ba su kuma yi musabaha ba a yayin bikin rattaba hannun, wanda ya dauki tsawon mintuna 50 ana yi.

 

Karin Bayani: An nada masu shiga tsakani a rikicin kasar Kwango