1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango da 'yan tawayen M23 sun amince da sulhu

Binta Aliyu Zurmi
November 15, 2025

Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango da 'yan tawayen M23 sun rattaba hannu kan wani sabon shirin samar da zaman lafiya da ya gudana a Qatar wanda ke da nufin kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a tsakaninsu.

Katar Doha 2025 | Waffenstillstandsabkommen zwischen Kongo und M23-Rebellengruppe
Hoto: Karim Jaafar/AFP

Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango da 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan kasar Rwanda sun rattaba hannu kan wani sabon shirin samar da zaman lafiya da ya gudana a Qatar wanda ke da nufin kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a tsakaninsu.

Qatar tare da Amurka da kungiyar Tarayyar Afirka sun shafe watanni suna tattaunawa kai tsaye da nufin kawo karshen wannan rikici na musamman gabashin Kwango mai arzikin ma'adinai, inda kungiyar M23 ta kwace wasu muhimman garuruwa.

Kwangon da M23 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma wani tsarin tun farko a Qatar a watan Yuli, amma duk da yarjejeniyar ta baya, an samu rahotannin karya doka, inda ake zargin bangarorin biyu suka bujire. 

An cimma sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a wani dan karamin biki da ya samu halartar wakilai daga bangarorin da ke gaba da juna da ma masu shiga tsakani Amurka da Qatar.


Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a wani farmaki da na mayakan M23 a watan Janairu da Fabrairu, inda suka kwace wasu muhimman manyan lardunan Goma da Bukavu.

Karin Bayani:Kwango da M23 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu