1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango: M23 ta karbe iko da mahakar ma'adinai ta Rubaya

May 2, 2024

'Yan tawayen M23 na ci gaba da kara matsawa zuwa arewacin Kivu tare da yin awon gaba da wasu muhimman maradun gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

DRC: M23 ta karbe iko da mahakar ma'adinai ta Rubaya
DRC: M23 ta karbe iko da mahakar ma'adinai ta Rubaya Hoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

'Yan tawayen M23 masu samun goyon bayan Ruwanda sun karbe iko da cibiyar hakar ma'adinai ta Rubaya da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango bayan gwabza kazamin fada, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar.

Karin bayani: Fargabar barkewar yaki tsakanin Ruwanda da Kwango

Wannan cibiya ta hakar ma'adinan sarrafa kayan latroni da ke yankin Masisi a lardin Kivu ta Arewa mai tazarar kilomita 40 da birnin Goma na zama daya daga cikin gurare masu matukar mahimmanci da gwamnatin Kwango ke tinkaho da su.

Karin bayani: Amirka ta yi Allah wadai da rincabewar rikici a Kwango

Wasu shaidu da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya yi hira da su sun ce tun a ranar Talabar da ta gabata ne 'yan tawayen suka shiga tsakiyar birnin bayan share wuni guda na bata kashi.

Wata jami'ar kiwon lafiya da ke yankin ta ce an samu asarar rayukan fararen hula uku da gwamman mayaka tare kuma da jikkatar mutane bakwai a yayin bata kashin da aka yi tsakanin 'yan tawayen da sojojin gwamnati.