Kwango: Mutane 200 sun mutu a ruftawar mahakar ma'adanai
January 31, 2026
Talla
A kalla mutane 200 ne aka bayar da rahoton sun gamu da ajalinsu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon ruftawar wasu mahakar ma'adanai a yankin Kivu a cewar wasu hukumomi da suke da alaka da 'yan tawayen M23. Wani mai magana da yawun gwamnan lardin na bangaren 'yan tawayen, ya ce wadanda suka mutu sun hada da masu hakar ma'adanai da yara da kuma mata 'yan kasuwa.
Karin bayani: Ruftawar mahakar ma'adanai ta kashe mutane 101 a Kwango
An ruwaito cewa, mahakar ma'adanan sun rufta ne a ranakun Laraba da kuma Alhamis. Kawo yanzu, gwamnan ya dakatar da hakar ma'adanai a wuraren, ya kuma bayar da umurnin kwashe mutanen da suka gina matsuganne a kusa da mahakar ma'adanan.