1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin ruwa ya halaka mutane a Kwango

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 15, 2023

Mahukunta a yankin Arewa maso Yammacin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun sanar da gano gawarwakin mutane 28 a kogin kasar yayin da wasu da dama suka yi batan dabo biyo bayan kifewar wani kwale-kwale.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Hadari | Kwale-Kwale | Mbandaka
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta saba fuskantar kifewar kwale-kwaleHoto: Junior Kannah/AFP/Getty Images

Mahukuntan na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun sanar da cewa kwale-kwalen ya tashi ne daga garin Mbandaka zuwa yankin Bolomba da ke Arewa maso Yammacin Kwangon, kafin ya kife ya kuma nutse cikin dare a ranar Jumma'ar da ta gabata.