1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango na maraba da tallafin rigakafin Mpox

September 6, 2024

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce jirgin dakon kaya makare da allurar rigakafin cutar kyandar biri zai isa filin jiragen sama na Kinshasa da ke Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango.

Wani mai dauke da cutar Mpox a Kwango
Wani mai dauke da cutar Mpox a KwangoHoto: WHO/Aton Chile/IMAGO

Cibiyar dakile cututtuka masu saurin yaduwa ta Afrika ta ce ana sa ran shigowar rigakafin sama da dubu 99,000, domin tunkarar rigakafin cutar ta kyandar biri gadan-gadan. Tuni dai jirgin ya bar birnin Copenhagen na kasar Denmark domin isa Jamhuriyar Kwango.

Karin bayani: Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika 

A wani taron manema labarai da ya gudanar shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya tabbatar da isar rigakafin na kamfanin Bavarian Nordic a matsayin gudummuwa daga kungiyar EU.

.