Kwango ta kira jakadanta a Libiya zuwa gida
November 22, 2017Talla
A cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar Léonard She Otekitundu ya fitar a ranar Talata ya bayyana cewa gwamantin na bukatar tattaunawa da jakadan domin sanin takamaiman abin da ke wakana a kasar ta Libiya, da ma duba yiwuwar kwaso 'yan kasar ta Kwango da ke a Libiya zuwa gida idan har ta tabbata cewa suna daga cikin mutanen da cinikin bayin ya shafa a kasar.
Da ma dai Burkina Faso ta kira jakadanta na Libiya zuwa gida a yayin da kasar Nijar daga nata bangare ta gayyaci jakadan Libiya a kasar domin bayar da bahasi, kana Shugaba Mahamadou Issoufou ya yi kira ga kotun kasa da kasa ta ICC da ta duba wannan batu na cinikin bayin a kasar ta Libiya.