An sake samun wanda aya kamu da Ebola a Kwango
May 14, 2018Talla
Jami'an kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na shirin kaddamar da ayyukan gaggawa na allurar rigakafi daga cutar Ebola, bayan da aka sake samun tabbacin barkewarta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango.
A cewar hukumar lafiya ta duniya wato WHO, kawo yanzu mutane 18 ne suka mutu daga cutar, yayin da ake fargabar wasu 35 da kamuwa da cutar.
A wannan mako ne hukumar za ta fara allurar rigakafi a kan iyakar kasar da sauran kasashe makotanta.