1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kwango za ta cire wa Kabila rigar kariya

Abdullahi Tanko Bala
May 1, 2025

Gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta kaddamar da yunkurin cire wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila rigar kariya.

Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyya Kwango Joseph Kabila
Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyya Kwango Joseph Kabila Hoto: Luis Tato/AFP

Fadar gwamnatin Kwango a Kinshasa ta yi zargin cewa akwai hujjoji da suka nuna Kabila na goyon bayan kungiyar 'yan tawayen M23 da ke samun tallafin kasar Rwanda wadanda suka kwace muhimmin birnin Goma da ke gabashin Bukavu da suka karbe a watan Fabrairu.

Ministan shari'a na Kwango Constant Mutamba ya ce mai gabatar da kara na sojoji ya mika wa majalisar dattijai bukatar cire wa Kabila kariyar da yake da ita a matsayin dan majalisar dattijai.

Mutamba ya ce gwamnatin Kwango ta na da kwararan hujjoji da suka tabbatar da cewa Kabila na da hannu a aikata laifukan yaki da keta haddin bil Adama da kisan fararen hula da kuma sojoji

Ya yi kiran Kabila ya dawo Kwango domin fuskantar hukunci ko kuma a yi masa shari'a a bayan idanunsa.

A shekarar 2023 Kabila ya yi gudun hijira don radin kai zuwa Afirka ta Kudu bayan samun sabani tsakaninsa da shugaba Felix Tshisekedi.

A 2024 Tshisekedi ya zargi Kabila da goyon bayan 'yan tawayen M23 da kuma haddasa yi wa gwamnati bore a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, zargin da Kabila ya musanta.