Kwango za ta fara karbar bakin haure da Amurka ta kora
April 7, 2026
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ta sanar da cewa za ta fara karbar bakin hauren da aka kora daga Amurka tun daga wannan watan Afrilu, a karkashin wata yarjejeniya da ta kulla da Washington.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda wannan tsari zai gudana ba, duk da cewa kasashen biyu na kuma tattaunawa kan yarjejeniyoyin hakar ma'adinai.
Amurka ta tura bakin haure zuwa Kamaru
Har kawo wannan lokaci babu wani jami'in gwamnatin Kwango da ya iya ba da cikakken bayani kan adadin mutanen da za a karba, balantana ribar da kasar za ta samu bayan da a ranar Lahadi da ta gabata fadar mulki ta Kinshasa ta sanar da amincewarta domin fara aiwatar da tsarin na wucin gadi.
A watannin baya-bayan nan dai kasashe da dama a nahiyar Afirka, ciki har da Equatorial Guinea da Ghana da Rwanda da Afirka ta Kudu da Sudan da Kamaru da kuma Eswatini, sun amince da wannan shiri na gwamnatin Trump na karbar bakin haure da ke zaune a Amurka ba bisa ka'ida a madadin ba su tallafin kudi ko kuma wasu kayayyaki.
Sai dai Burkina Faso da ke yankin Sahel kuma karkashin mulkin sojojin ta yi watsi da wannan tsari na gwamnatin Amurka, yayin da wasu kasashen Afirka ke nazartar tayin da Washington ta yi musu.