1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwankwaso ya kaddamar da takara a APC a 2015

Ubale Musa daga AbujaOctober 28, 2014

Gwamnan Kano Dr.Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana aniyarsa a babban birnin tarayyar Najeriya ta neman tsayawa takara a zaben shugaban kasa a 2015 karkashin inuwar jam'iyyar APC mai adawa.

Rabiu Musa Kwankwaso
Hoto: DW/T. Mösch

Dubun dubatar magoya bayan gwamnan jihar Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso sun tattaru a Abuja dan nuna masa goyon bayansu, a aniyar da ya bayyana na kasancewa daya daga cikin masu bukatar neman tsayawa jam'iyyar APC ta adawa takara a zaben shugaban kasa.

Babbar damuwa cikin jam'iyyar na zaman rabuwar kai a tsakanin bangarorin jam'iyyar, dake iya yin illa ga makomar APC da a karon farko ke kallon nasara a cikin yakin kai karshen mulkin PDP na shekaru 16.

To sai dai kuma a fadar Senata Kabiru Gaya dake zaman na gaba ga masu tabbatar da takarar ta Kwankwaso dai na ganin hakurin manyan jam'iyyar irin na su Buhari da Atikun dai na zaman mafita ga kokarin kai jam'iyyar ga tudun mun tsira.

Hoto: AP

“Muna fada cewa ragowar 'yan takarar, yayyanmu sun cancanta, amma su kyale Rabi'u Musa Kwankwaso shi ne matashi da sauran jini a jiki wanda zai yi wannan takara da yardar Allah”

Shi kuwa Senata Bindo Jibrilla dake zaman me goyan baya ga Atiku ya nuna shirinsu na goyon baya ga duk wanda jam'iyyar ta kai ga fitarwa.

Zuwanmu wannan taro ma da yardar mai gidanmu muka zo. Mu abin da muke kiransu manya, da su hada kai su fitar da mutun daya, duk wanda suka fitar ya isa ya rike kasar nan, kuma duk wanda suka fitar ya isa ya kuma taimaki talaka, kuma duk wanda Allah ya bawa zamu yi masa biyyaya

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani