1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'a na guduwa daga Chadi saboda fargaba

April 22, 2021

Daruruwan jama’a na ta fitowa daga Chadi zuwa wasu garuruwa a gabar tafkin Chadin saboda fargabar tashin hankali bayan rasuwar shugaban kasar Idriss Deby Itno 

Pressefoto UNHCR | Tschad, Hilouta
Hoto: UNHCR/Aristophane Ngargoune

Tun lokacin da ‘yan tawayen Arewacin kasar Chadi suka tunkari N’djamena fadar gwamnatin kasar da ma bayan samun labarin kashe marigayi shugaba Idris Deby hankulan wasu ‘yan kasar ya kasa kwanciya saboda fargabar barkeraw rikici. Wannan ya sa da yawan su tserewa zuwa yankuna da garuruwan da ke bakin gabar tafkin Chadi cikin kasashe makobta domin neman mafaka.

Cincirindon mutane sun shiga kasashen Najeriya da Njiar da kuma bangaren jamhuriyar Kamaru domin guje wa tashin hankali ganin ‘yan tawaye na ci gaba da dannawa zuwa N’djamena fadar gwamnatin kasar. 

Karin Bayani: Kokarin sake tsugunar da 'yan gudun hijira na tafkin Chadi

Hoto: picture-alliance/dpa

Masana na nuna fargabar ‘yan ta’adda za su iya fakewa cikin masu gudun hijirar kuma za a iya shigar da makamai a irin wanann yanayi.

Kwamarade Dauda Muhammad shugaban gamayyar kunyoyin matasa da ke son kawo ci gaba a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya yace akwai faya fayen bidiyo da ke karada shafukan sadarwa na zamani da ke nuna yadda ‘yan kasar Chadin ke kwarara sassan kasashe makwabta abun ya kara tada hankulan mutane.

Hoto: AP

Dr Umar Adamu Malami ne a Jami’ar jihar Gombe ya ce ya zama wajibi gwamnatocin kasashen da ke kewaye da Chadi su tashi tsaye su magance matsalar kwararar ‘yan gudun hijira.

Talakawa da ke yankin sun a ajiye dukkanin banbance banbance na addini ko siyasa tare da yin addu’oi domin neman Allah ya kawo musu dauki.

 Alh Ibrahim Wazana wani mazaunin yankin Arewa maso gabashin Najeriya ne yace yanzu haka hankula sun karkata kan yadda shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da Jamhuriyar Kamaru gami da kasashen Afirka ta tsakiya za su yi su magance duk wata barazana da ka iya bullowa game da kalubalen tsaro.