Kwararru daga MDD za su binciki rikicin Hamas da Israila
August 11, 2014MDD ta bayyana sunayen wasu kwararru 3 da zasu yi aiki a hukumar kasa da kasa da zata duba wasu laifukan yaki da bangaren Hamas da Israila suka tafka a yankin Gaza.
William Schabas wanda farfesane a harkokin sharia daga Canada shi zai jagoranci tawagar kwararun da mambobinta suka hada da Doudou Diene sanannan mai fafitikar hakkin bil' adama daga kasar Senegal da Amal Alamuddin wani lauya dan asalin Birtaniya da Lebanon.
Wannan tawagar kwararru dai zata yi aikine dan bincikar duk wasu dokokin kasa da kasa da aka tanada dan kare hakkokin jamaa dasojoji suka take su a lokacin gwabza fada tsakanin bangarorin biyu.
A watan Maris na shekarar 2015 ne ake saran kwararrun zasu mika rahoton su ga cibiyar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya. Rahoton mambobin kasashe 47 da Israila ke cewa ba zai zamo sahihiba.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba