1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwararu daga Hukumar Lafiya sun isa Wuhan

Binta Aliyu Zurmi
January 14, 2021

A wannan rana ta Alhamis tawagar kwararru daga Hukumar Lafiya ta Duniya suka sauka a birnin Wuhan na kasar Sin domin gudanar da binciken musabbabin yaduwar cutar corona wacce ta samo asali daga kasar ta Chaina.

China Coronavirus WHO Flughafen Wuhan
Hoto: Ng Han Guan/AP Photo/dpa/picture alliance

Tawagar ta mutum goma dai za ta kwashe tsawon makonni biyu tana killace, amma za su fara gudanar da bincikensu ta kafar bidiyo da takwarorinsu na Chaina, kafin daga bisani a gudanar da gwajin cutar a kansu.


Hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO ta kwashe watanni tana bin mahukuntan na Beijin domin ba da izinin fara wannan binciken.

Masana na zargin wannan cuta wadda ta samo asali daga Jemage ya zuwa yanzu ta janyo hasarar rayukan mutane sama da mutum miliyan daya da dubu dari tara.