1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gyaran kundin tsarin mulki

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 7, 2022

Kwamitin sauye-sauyen tsarin mulki a Najeriya, ya kammala daidaita sassan da aka yi wa gyaran fuska domin ganin an amince da su don kyautata al'amura.

Najeriya| Majalisar Dattawa
Majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya, na son kammala gyaran kundin tsarin mulkiHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Muhimmai daga cikin abubuwan da suka amince da su din dai su ne: bai wa kanana hukumomi 'yancin cin gashin kansu da kuma kebe kaso 25 na kujeru a majalisar dokokin Najeriyar ga mata. 'Yan majalisar dokokin Najeriyar sun kwashe tsawon kwanaki biyu, suna daidaita sassan kundin tsarin mulkin kasar da aka yi wa gyaran fuska domin samun daidaito kan abubuwan da aka amince da su tsakanin majalisar dattawa da na wakilai. Sassan da aka yi wa gyaran fuskar sun kai 55. Majalisar dokokin Najeriyar dai ta dade tana fadi tashin ganin an bai wa kananan hukumomi 'yancinsu, Sai dai har kawo yanzu abin ya ci tura.
Koda majalisa ta takwas an yi wannan kokari sai dai abin yaci tura kasancewar tilas sai an samu kaso biyu bisa uku na majalisun jihohi sun amince kafin aiwatar da sauyin. A sabuwara dokar da aka yi wa gyaran fuskar dai, an kebewa mata kujerar sanata guda a kowace jiha tare da ta 'yan majalisar wakilai guda biyu. Wannann dai ya sanya su doki, kasancewar sun dade suna neman karin mukaman siyasar da a yanzu kaso uku cikin 100 kacal suke da shi a majalisar dokokin kasar. An dade ana nuna dan yatsa a kan kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da wasu ke wa kalon sojoji ne suka tsara shi kafin sake kafa mulkin dimukuradiyya, abin da ya sa yake fuskantar gyare-gyare.

Majalisar dokokin Najeriya, na son kammala gyaran kundin tsarin mulkin kasarHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani