1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwaskwarima a dokar filayen noman Zimbabwe

Zainab Mohammed Abubakar/PAWMay 26, 2015

Shugaba Robert Mugabe ya gyara dokar da ta tanadi mayar da filayen gonar kasar mallakar bakaken fatar Zimbabwe, domin anshewa daga hannun fararen fata.

Robert Mugabe in Südafrika
Hoto: picture-alliance/dpa//Government Communication and Information System (GCIS)

Shekaru 15 bayan garon bawul ga wannan doka ta mallakawa babaken fatar kasar filayen da a baya fararen fata ne ke nomasu, Zimbawe ta wayi gari cikin halin kaka ni kayi na ciyar da kanta balle kasashe makwabta, da ke dogaro da ita wajen samun abinci a yankin kudancin Afirka, kamar yadda Prosper Matondi, babban darektan wata gidauniyar amintattu da ake kira Ruzivo dake babban birinin kasar watau Harare ya shaidar...

" Ya ce kafin wadannan gyare gyaren, Zimbabwe na samar da sama da kayayyakin gona 26 a kasuwannan kasashen yankin, amma yau an wayi gari babu wadannan kayayyakin, karshenta ma shigowa muke da kayan abinci daga ketare".

Sama da shekaru 16 kenan wannan gidauniya ta Ruzivo da ke yaki da matsalolin da sashinj noma na kasar ta Zimbabwe ke fuskanta, kasar da abaya ake bayyanata da kasancewa rumbun abincin kudancin Afirka.

Noma ginshikin rayuwar talakan Zimbabwe

Sashin noman dai shine ke bada kashi 40 daga cikin 100 na kuadaden shigar kasar, saboda manomanta na fitar da abincin da suka noma zuwa kasashen da ke makwabtaka domin sayerwa. An wayi gari sai Zimbabwe ta shigo da Masara da kayan marmari na itatuwa da sauran kayan abinci daga ketare. Manazarta kamar Matondi na dora alahakin wannan matsala akan gwamnati.

A shekara ta 2000 ne dai shugaba Mugabe ya kadddamar da wannan shiri na gaggauta sauya dokar mallakar filaye. Batun da ya juya sashin noma na kasar. A shekaru 15 da suka gabata dai an rarraba wa bakaken fata filayen noma sama da Hectoci miliyan 7, wanda gwamnati ta ce a madadin mulkin mallaka ne da aka yi musu a baya.

Taba na daga cikin manyan abubuwan da ake nomawa a ZimbabweHoto: AFP/Getty Images

A shekara ta 2000 aka aiwatar da wani bangaren dokar

Akan wannan shiri ne aka tilasta wa manoma fararen fata wajen dubu 4 da 500 barin gonakinsu, wadanda aka gutsuttsura aka rabawa sama da bakake miliyan guda, akasarinsu kananan manoma da wadanda ke da alaka da gwamnatin Mugabe. Kamar yadda masanin kimiyyar siyasa Phillan Zamchiya da ke koyarwa a Harare da Oxford ya nunar...

" Ya ce ba zamu iya kawar da kai wajen nunar da cewar akwai rashin kyakkyawar gudanarwa, saboda gwamnatin bata da masaniya kan irin tsare tsaren da zata fitar domin alkinta tattalin arzikin kasa. cin hanci da karbar rashawa ya mamaye sassa daban daban na tattli da sauransu".

Tun bayan haka ne tattalin arzikin Zimbabwe ya fara durkushewa. Kashi 80 daga cikin 100 na al'ummar kasar na rayuwa cikin talauci. Bakaken fata wajen dubu 300 da ke aiki a gonaki ne suka rasa ayyukansu tun bayan kaddamar da dokar.

Ma'aikatan gona da dama sun rasa aiki a dalilin wannan dokaHoto: DW

Daura da haka ba'a biya fararen fatar kasar kudaden gonakinsu da aka kwace ba. Sashin noma na kasar na dogaro da goyon bayan manoma ga jam'iyyar ZANU-PF mai mulki, idan baka tare da su zaka fuskanci cin zarafi, tozartawa a wasu lokuta har da duka. Kuma a siyasance ne kadai ake iya warware matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki.