1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyaftin Traore ya ce a kwantar da hankali

Abdourazak Maila Ibrahim MAB
October 4, 2022

Sabon shugaban mulkin Sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya bayyana "takaicinsa" dangane da kiraye-kirayen kawo cikas ga ziyarar da tawagar kasashen yammacin Afirka za ta yi a birnin Ouagadougou a ranar Talata.

Lage in Burkina Faso I 2. Oktober 2022
Halin da ake ciki a Burkina Faso bayan da Kyaftin Ibrahim Traore ya yi juyin mulkiHoto: Vincent Bado/REUTERS

Kyaftin Traore ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewar wannan aikin na ECOWAS ko CEDEAO, ana yin sa ne don tuntubar sabbin mahukuntan Burkina Faso a matsayin wani bangare na tallafin da kasashen yammacin Afirka suka bayarwa.

A daren Litinin zuwa wannan Talata ne wasu kungiyoyi suka kafa shingaye a tsakiyar birnin Ouagadougou domin nuna adawa da zuwan tawagar kungiyar ta ECOWAS. Sannan, an ta yada sakonni a shafukan sada zumunta ne neman kawo wa ziyarar cikas. Dama kungiyar ECOWAS ta saba shan suka a kasashen yammacin Afirka bisa ga tsarinta idan aka yi juyin mulki ba tare da la'akari da muradun jama'a ba.

Sai dai  Kyaftin Traore ya yi alkawarin mutunta alkawuran da magabacinsa ya yi wa kungiyar ECOWAS kan shirya zabe da kuma dawowar farar hula kan karagar mulki nan da watan Yulin 2024.