Kyakkyawan fata ga jagoran 'yan adawa a Senegal
March 23, 2012Za mu fara ne da ƙasar Senegal inda a labarin da ta buga mai taken Macky Sall jagoran 'yan adawa a Senegal da fatan da matasa ke yi jaridar Süddeutsche Zeitumg ta fara da cewa:
"Duk mai son canji yana goya masa baya, saboda haka Macky Sall na da kyakkyawar damar lashe zaɓen shugaban ƙasar Senegal zagaye na biyu da ake gudanarwa a wannan Lahadi. Da yawa daga cikin 'yan ƙasar za su zuba ruwa a ƙasa su sha idan Sall mai shekaru 51 ya kai gaci, domin tun wasu watanni kenan ƙasar dake yankin Yammacin Afirka ta shiga mawuyacin hali ƙarƙashin sakamakon take-taken shugaba Abdoulaye Wade."
Rikicin 'yan tawaye a Mali ya yi muni
Wani sabon yaƙi a Hamada na ƙara yin muni a tsakiyar Sahara inji jaridar Die Tageszeitung tana mai nuni da yadda yankuna da dama na ƙasar Mali ke faɗawa hannun 'yan tawayen Abzinawa da kuma sojojin sa kai na Islama.
"Abin da ya fi mamaye kanun labarun jaridun ƙasar da ma a tsakanin al'uma tun gabanin juyin mulkin soji a Mali shi ne yaƙin da ya ƙi ya ƙi cinyewa a arewacin ƙasar tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen ƙungiyar 'yanto Abzinawa ta MNLA. A kullum wannan yaƙi yana ƙara bazuwa wasu yankunan ƙasar abin da ya tilasta ƙaurar dubun dubatan mutane zuwa ƙasashe maƙota. A ranar Talata wata ƙungiyar dake kiran kanta Ansar Dine wato mai kare addinin Islama ƙarƙashin jagorancin tsohon madugun Abzinawa Iyad ag Ghali ta yi iƙirarin kame garin Tessalit dake arewa maso gabacin Mali. Jaridar ta ce hakan na zuwa a daidai lokacin da aka kame shugaban ƙungiyar 'yan tawayen Abzinawa na MNJ Aghali Alambo.
Faɗaɗa aikin tsaron gaɓar tekun Somaliya
Matakin tallafa wa Somaliya inji jaridar Süddeutsche Zeitung a lokacin da take yaba wa ƙudurin tarayyar Turai na faɗaɗa aikin jiragen sama masu ungulu da za su dake shawagi a gaɓar tekun Somaliya domin fatattakar 'yan fashin ruwa.
"A siyasance wannan matakin zai yi ma'ana kuma taimakon da EU ke bayarwa na horas da jami'an tsaron Somaliya da tallafa wa aikin rundunar tarayyar Afirka ya zama kyakkyawar alamar ga dakarun kiyaye zaman lafiya a Somaliya cewa ba a ƙyale su su kaɗai ba.Sai dai idan Turai na samun ta samu nasara to dole ta guji yin abin da zai janyo salwantar fararen hula da ba za su hawa ba su san sauka ba, idan ba haka ba ƙaiƙayi zai koma kan masheƙiya."
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta mayar da hankali ne akan rawar da manyan kantuna ke takawa wajen shigar da ƙananan manoma a haɗakar kasuwanci.
"Matsalolin manoman Afirka ke fuskanta a wasu ɓangarori sun yi kama da na takwarorinsu na Turai wato rashin tabbas game da yanayi, ƙarancin ruwan sama, yayin da taki da kuma makamashi ke ƙara yin tsada. Ban da nan babu wata danganataka. Yayin da manomi a Turai ke murnar girbar kayan amfanin gonansa saboda zai iya sayar da su ba da matsala ba, manomin Afirka kuwa sai ya sha da ƙyar kafin ya iya kai hajjarsa kasuwa. Har in dai za a yi musu adalci kuma ba za a karya farashi ba, to matakin da manyan kantuna ke shirin ɗauka na shigar da ƙananan manoman a cikin harkokinsu zai share musu hawaye.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar