Fatar samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
October 13, 2025
.
Dazu da rana ne kungiyar Hamas ta sako mutane 20 da ta yi garkuwa da su shekaru biyu da suka gabata, ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wutar da Amurka ta ƙulla, a wani babban mataki da ake ganin zai kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe shekaru biyu ana yi a Gaza da ya laƙume rayukan dubun dubatar Falasɗinawa.
Musayen fursunoni
Zaratan mayakan Hamas 12 ne, cikin cikakkaiyar damararsu, sanye da bakaken kaya fuskoki rufe, suka mika 'yan Isra'ilan ga kungiyar agaji ta Red Cross a yankin Khan Yunus da ke tsakiyar birnin na Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta karbi duk mutanen da aka yi garkuwa da su, waɗanda ƙungiyar agaji ta Red Cross ta yi jigilarsu daga Gaza zuwa inda iyalansu ke dakon ganinsu a Tel Aviv, inda su ka riƙa rungumar juna ana kukan farin cikin yaushe gamo.
A nasu bangaren, Fursunonin Falasɗinawa da Isra'ila ta sako a wani bangare na yarjejeniyar sun isa Zirin Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, inda aka hango su kawunansu a aske, wasu kuma daga ciki sun kasance a rame sosai.
Taron zaman lafiya
Duk hakan dai na zuwa ne, lokacin da shugabanin duniya suka gama taron murnan cimma yarjejeniyar zaman lafityar na Gaza a birnin sharm alsheikh na Masar,inda shugaban Amurka ya siffanta wannna zaman
Bayan ga Masar din dai shugaban na Amurka ya isa Isra'ila inda yayi jawabin godiya a majalisar Isra,ila yana mai jinjinawa Natenyahu kan hadin kan da ya bayar har akai nasarar cimma yarjejeniyar kamar yadda ya nemi majalisar da tai mar afuwa kan tuhume htuhumen cin hanci da rashawar da ake masa.
A daura da haka,adaidai lokacin da motocin agaji ke ta yin tururuwa zuwa zirin na Gaza, masu aikin kwana-kwana sun nemi agajin gaggawa na share hanyoyi da titinan dake cike da buragujen rusau,don a samu kayyakin agajin su isa wararen dake toshe.