1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyakkyawar maraba ga wakilan MƊD a Siriya

April 16, 2012

Rukunin farko na masu sanya idon MƊD sun isa birnin Damascus na Siriya a ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin ƙasar

A team of U.N. monitors walk through a hotel in Damascus April 16, 2012. A United Nations advance observers' team arrived in the Syrian capital Damascus late Sunday to monitor the fragile cease-fire brokered by international envoy Kofi Annan, causing discussion from all circles in Syria. REUTERS/Khaled al- Hariri (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY POLITICS)
Ayarin farko na MƊD a SiriyaHoto: Reuters

A wannan Litinin ce hukumomin Siriya suka marabci rukunin farko na tawagar masu sanya ido na Majalisar Ɗinkin Duniyar da suka isa ƙasar domin kula da yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar dake tangal-tangal, a dai dai lokacin da dakarun gwamnatin ƙasar ke ci gaba da yin luguden wuta akan birnin Homs dake zama ɗaya daga cikin wuraren da 'yan adawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na ƙasar ta Siriya ke da ƙarfi. Masu fafutuka suka ce wannan shi ne faɗa mafi tsanani tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ita.

An dai tsara cewar rukunin farko na masu sanya idon daya ƙunshi mutane shidda zai gana tare da ministan kula da harkokin wajen Siriya a wannan Litinin, kana zai fara ne da yada zango a birnin na Homs. Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya buƙaci mahukunta a birnin Damascus na Siriya da su mutunta yarjejeniyar:

" Ya ce yana da muhimmancin gaske gwamnatin Siriya ta ɗauki matakan dakatar da tashe-tashen hankula, kuma ina matuƙar nuna damuwa da irin abubuwan da suka afku daga jiya zuwa yau."

A wannan Asabar ce kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da tura wata tawagar masu sanya idon da ba ta da makamai mai wakilai 30. Ƙudirin tura tawagar dai shi ne na farkon da kwamitin sulhun mai ƙasashe mambobi 15 ya amince da shi tun bayan ɓarkewar rikicin na Siriya a cikin watan Maris na shekara ta 2011.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas